Labarai

Ganduje Ya Kira Shugaba Buhari A Waya Kowa Ya Ji

A yau ne aka gudanar da wani gangamin addu’a a fadar gwamnatin Kano don yi wa Sgugaba Muhammadu Buhari da Nijeriya addu’a.
Gangamin da ya hada manya-manya Malamai da Alarammomi ya samu halartar gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a matsayin mai masaukin bako da kuma mataimakinsa da wasu da dama daga jami’an gwamnati

A yayin taron ne dai gwamna Ganduje ya kira Buhari a waya kuma ya bude muryarta ta yadda mutanen da suke dakin taron suka ji murya Shugaba Buhari
Buhari ya yi godiya ga taron malaman da suka yi masa addu’ar tare kuma da tabbatar musu da cewa yana cikin koshin lafiya

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.