-Advertisement-


GANDUJE YA KADDAMAR DA BADA TALLAFIN CORONA


0 660

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya kaddamar da shirin Gwamnatin sa na bada tallafi ga masu bukata a fadin jihar Kano domin rage radadin da ake fama da shi bisa barkewar cutar Corona wato Covid-19 a Jihar.

Kayan tallafin wanda kwamitin neman tallafi da Gwamnati ta kafa karkashin jagorancin Farfesa Yahuza Bello ya tara kudi da kayan abinci daga masu kudi da kuma kamfanunnuka suka tara, sannan Gwamnatin jiha ta cika, kuma yau aka fara rarrabawa ga kananen hukumomi guda 8 dake cikin birnin Kano kuma zaa bawa magidanta 50,000 a karo na farko.

Ana sa ran zaa rabawa magidanta dubu dari uku (300,000) a fadin jihar kuma kayan da kowanne magidanci zai samu sun hada da buhun shinkafa ko kuma na samovita da kwallin makaroni ko na taliya ko na indomie da man gyada gallan daya da kuma kudi N2,000. Ko wacce mazaba zaa dauki mutum 4 a kowacce rumfar zabe ta mazabar.

A kowacce karamar hukuma, Hakimi shi ne jagoran kwamitin raba wannan kaya da shugaban karamar hukuma da zai tallafa masa, sannan akwai Dagatai da masu unguwanni a cikin kwamitin da kuma sauran masu ruwa da tsaki.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 608

-Advertisement-

Sannan rukunin wanda zasu ci gajiyar wannan tallafi sune marasa aikin yi wanda basa daukar albashi, mutanen da ba sa aiki ko a matakin Gwamnatin taraiya ko Gwamnatin jiha ko kuma kanamar hukuma. Haka duk mai aikin kamfanunnuka masu zaman kan su baya ciki, da kuma masu sana’a. Tallafin na marasa galihu ne wanda basu da aikin komai kuma basu da hanyar samun abinci.

Gwamnatin ta na kara kira ga mutane da a ci gaba da kiyayewa da ka’idojin da likitoci da kuma hukumar NCDC suka shinfida domin kare kai daga kamuwa da cutar Corona wato Covid-19.

Salihu Tanko Yakasai
Special Adviser Media
Government House Kano
April 23, 2020.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.