Ganduje Ya Dakatar Da Mai Taimakamasa Kan Kafafen Yada Labarai Saboda Caccakar Buhari


0 357

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya dakatar da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Salihu Tanko Yakasai kan wani rubutu da ya wallafa a shafin sada zumunta inda ya soki yadda gwamnatin Buhari ta gudanar da zanga-zangar #ENDSARS.

Yakasai ya wallafa a shafinsa na Tweeter cewa, “Ban taba ganin gwamnatin da ba ta da tausayi irin na shugaba Buhari. Sau da yawa, lokacin da jama’arsa ke cikin mawuyacin hali kuma suna tsammanin wani irin bugawa a kafaɗa don tabbatar musu cewa shi ke shugabanta, amma ya kasa yin haka.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 627

-Advertisement-

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Muhammad Garba ne ya sanar da dakatar da Yakasai.

“Duk da cewa mai taimakawa a kafafen yada labarai ya mallaki  ra’ayinsa na kashin kansa, amma hakan a matsayinsa na jama’a, zai yi wahala a banbance tsakanin ra’ayin mutum da matsayin hukuma kan al’amuran da suka shafi jama’a,” in ji shi.

Sanarwar ta kara da cewa “Don haka gwamnan ya gargadi wadanda aka nada a mukaman siyasa da ma’aikatan gwamnati da su kiyaye yin maganganun da za su iya haifar da takaddama da ba ta dace ba.”

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.