Gwamann Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya shigar da karar kamfanin jaridar DAILY NIGERIAN tare da mawallafin jaridar Jaafar Jaafar, akan neman diyyar Naira biliyan 3 saboda laifin fallasa bidiyon da ke nuna cewa, Gwamnan na karbar cin hanci daga hannun ‘yan kwangila.
- Advertisement -
Jaridar DAILY NIGERIAN ta fitar da rahoton cewa, babbar kotun jihar ne ta sanar da hakan wata daya kenan bayan fallasa bidiyon.