Game Da Shirin Film Din Labarina, Gaskiya Akwai Gyara Akan Saka Sunan Mahmud Amatsayin Sunan Maciyi Amana

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Ibrahim Dau Mutuwa Dole

Masu Shirya Film din labarina Kun Shirya Cewa Mahmud Zaiyi Butulci Da Cin Amana Acikin shirin naku.

Amma Sai Nake ganin Baikamata Ayi Amfani Da Suna Mai Daraja ba wajen Baiwa Maciyi Amana, saboda Ba halin Mai sunan Bane.

Dayawa Daga Cikin Masu Kallon Film din Suna Maganganu Marasa Dadi Akan Mai Wanda aka sakawa sunan Mahmud Musamman Mata, Suna Jifar Mahmud da Munanan Kalamai Marasa Dadi Batare Da Sunyi La’akari da Muhimmancin Sunan Ba Wajen sukarsa Da Kalamansu ba.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 12

To Gaskiya Sai nake ganin Kamar Amfani Da sunan Mahmud Amatsayin Maciyi Amana Hakan Kamar Akwai kuskure aciki Domin kuwa Suna ne Mai Daraja.

Da Wannan Nake kira Ga Mahukuntan Dake shirya Wannan Shirin Akan ya kamata A sauya Sunan Mahmud izuwa wani sunan Na Daban.

Ina Mai fatan Za’a Gyara Domin Nunawa Makiya Manzan Allah S.a.w Cewa Sunan lallai Sunan Annabin mu Muna Kishinsa sosai Fiye Da komai Namu.

Allah Ya Bamu Ikon Gyarawa Amin.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: