Daga Abdulrashid Abdullahi, Kano
Gamayyar jam’iyyun siyasa sama da 40 za su marawa dan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar baya a zaben 2019.
Jamiyun sun dunkule waje daya domin taimakawa babbar jam’iyyar hamayya ta PDP wajen karbe kujerar shugabancin kasa daga hannun jam’iyyar APC mai mulki.
Shugaban gamayyar kuma tsohon Gwamnan jihar Osun Olagunsoye Oyinlola ne ya bayyana hakan a babban birnin tarayya Abuja a lokacin da gamayyar jam’iyyun suka yi babban taronsu.
Jam’iyyun da suka zabi Atiku a matsayin dan takararsu sun hada da AA, DPC, PANDEL, LP, MPN, ADC, AGAP, PPP, da dai sauransu.