-Advertisement-


Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Gabatowar Azumi: Mansurah Isah Ta Shirya Taron Koya Wa Mata Girki


0 936

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Tsohuwar jarumar fim kuma a yanzu take shugabantar Gidauniyar tallafa wa mata da marassa galihu wato “Today’s life foundation”  Mansurah Isah ta shirya wani taro na wuni 2 domin koya wa mata girki musamman ma dai a wannan lokaci da ake gab da shiga watan Azumi na Ramadan.

Taron wanda aka shirya kuma aka gudanar da shi a ranar  asabar 28 da lahadi 29 ga watan Afrilu an yi shi ne a dakin taro na Ahmed Musa Sport dake unguwar Hotoro a cikin garin Kano.

A wajen taron dai an koyar da mata abinci masu yawan gaske wadanda ya kamata su rinka shirya wa mazajen su a cikin azumi domin kara dankon soyayya a tsakanin su.

Cikin irin abincin da aka koyar sun hada da na kasar India da na kasashen larabawa da na turawa, kuma an koyar da girki irin namu na gida musamman wanda a irin na Hausawa ba ta yadda matan Hausawa za su rinka burge mazajen su da girke girke na musamman.

Sannan an koyar da yadda maya za su rinka hada lemo cikin sauki saboda lokacin shan ruwa.

Su ma yara ba a bar su a baya ba, don kuwa an koyar da mahalarta taron yadda za su hada abincin jarirai da sauran yara da suke da karancin shekaru.

Haka nan masu hawan jini da masu ciwon suka su ma an koyar da yadda za a hada musu abinci don gudun fadawar su cikin matsala.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 329

- Advertisement -

A kalla dai a wajen an koyar da hirke girke wajen  guda 50 a cikin wuni 2 da aka yi ana yin taron  kuma da alama matan da suka halarci wajen sun gamsu da tsarin da aka bi wajen koyar da su don kuwa sun tashi cikin farin ciki daga taron.

Su ma ‘yan fim ba a bar su a baya ba wajen halartar taron don kuwa da dama daga cikin su da su aka yi wuni 2 ana koyar da su.

Cikin wadanda suka je akwai Wasila Isma’l, Sadiya Gyale,Fati Al’men,Jamila Gamdare, Bilkisu Jibril, Asma’u Musa, Asma’u Sani, Halisa Muhammad,da sauran su.

Ko da wakilin mu ya tambayu Mansurah Isah dalilin ta na shirya wannan taro musamman ganin kungiyar ta tana bada tallafi ne ga marayu da marassa karfi, sai ta ce” To daman ita gidauniyar da nake shugaban ta ta hada duka ne har da samar wa mata aikin yi da sana’a don haka ne muka yi hadin gwiwa da kamfanin Raico muka shirya wannan taron.

Kuma mun zabi wannan lokacin saboda ana gab da shiga Azumi kuma ka san da yawa mata su abin da suka sani da azumi kawai shi ne a dafa shinkafa sai doya da dankali don haka ne kuma fito da wannan tsarin don mu nuna wa mata cewar akwai abinci masu yawan gaske da ya kamata a ce ana shirya wa maigida da sauran jama’a kuma daga yadda dakin taron ya cika a rana ta farko da ta biyu, alama ce da ta nuna mata sun karbi shirin da gaske.

Kuma wannan ne na farko muna fatan nan gaba za mu kara shirya wani taron domin kara koyar da mata wasu abubuwan. Allah ya saka wa kowa da alheri da fatan kowa zai koma gidan sa lafiya” inji Mansurah Isah.

#Hausaleadership

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.