Ga Dukkan Alamu Karshen Rashin Tsaro Ya Zo Karshe A Nijeriya


0 123

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Anas Saminu Ja’en

Inda a makon daya shude Sheikh Dr. Abdallah Umar Gadon Kaya ya fitar da wani faifan Bidiyo wanda fara fallasa tare da tonon silili kan irin kisan kiyashin da ake yiwa al’ummar jihar Zamfara kuma ya ce akwai saka hannun manya a ciki saboda bukatun kan su kuma Malam ya ce lokaci bai yi da za su bayyana sunayan su ba, Allahu Akbar wannan Bidiyo ya tunawa mutane sun tuna da Marigayi Malam Jafar Mahmud Adam da Sheikh Albani Zaria wadanda suka rasa rayukan su a irin wannan jihadin da Malam ya yi Allah ya gafarta musu ya bawa Malaman mu ikon fadar gaskiya.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 607

- Advertisement -

Kwatsam shima Ministan tsaron Najeriya Mansur Dan Ali ya kata jadda wannan abu inda ya ce akwai sasu masu rike da sarautun gargajiya, da suke taimakawa ‘yan ta’adda da bayanan sirri domin samun saukin kai hare-hare da kashe kashen dake faruwa a Arewa musamman a jihar Zamfara.

Tabbas wadannan furucin na mutane biyu suka Malam da kuma Ministan tsaro ya kara kwantar da hankulan ‘yan kasa musamman yadda gwamnati ta dauki tsattsauran mataki na kawo karshan duk wani lamari daya shafi tsaro, bisa irin kokarin da wasu daga cikin jami’an tsaro suke yi wajan wayar da kawunan al’umma da suke yi, kamar irin su Birgediya Janar SK Usman mai ritaya da Abba Kyari da Datti Assalafiy da sauran su wadanda suke sirrice da wadanda Allah bai bayana su ba ciki har da ‘yan uwa marubuta daga nan Arewa masu kishin yankin su da al’ummar su.

Muke ganin cewar Allah ya shigo cikin lamarin nan harkar ta’addaci ta kusa zuwa karshe a fadin Najeriya duba da yadda su kansu ‘yan ta’addar, kuma suna tserewa domin neman mafaka a wasu wurare sakamakon irin ragargazar da jami’an tsaron kasar nan ke musu, Allah ya taimaki shugabannin mu da sauran hazikan jami’an tsaron mu masu kishi, Allah duk wanda yake da sa hannu a rashin zaman lafiyar kasar nan Allah ya tona musu asiri tundaga nan duniya.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.