Wasanni

Ga Dukkan Alamu Kane Zai Kaurace Wa Tottenham Idan Ba A Sayar Da Shi Ba

advertisement

Wasu rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, Harry Kane, kuma kaftin din tawagar ‘yan wasan kasar Ingila zai kauracewa komawa kungiyar daukar horo idan har ba a sayar da shi ba ga kungiyar da take zawarcinsa.

Duk da cewa sabon kociyar kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, Nuno Espirito Santo, ya ce babu wata tattaunawa da suka yi tsakaninsa da kaftin din kungiyar, a kan zaman kungiyar ko kuma komawa wata kungiyar.

Santo ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da manema labarai sai dai ya ce yana fatan dan wasan, zai hakura domin ci gaba da zama a birnin na London har zuwa karshen kakar wasa mai zuwa.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City dai tuni ta kai tayin kudi har fam miliyan 100 domin sayan Kane sai dai nan take shugaban gudanarwar kungiyar ta Tottenham, Daniel Leby, yayi fatali da tayin kuma ya ce har yanzu yana fatan shawo kan Kane.

Manchester City da ta bayyana cewa tana mutukar bukatar dan wasan gaban na Ingila mai shekaru 27 a duniya, duba da yadda kociyan kuniyar, Pep Guardiola ya zaku ya sanya shi a cikin tawagarsa da ta lashe gasar Firimiya ta kuma kai wasan karshe na zakarun nahiyar Turai.

Harry Kane dai kawo yana da sauran kwantiragi da kungiyar Tottenham da zai kai har shekarar 2024 amma ya sanar da shugaban kungiyar, Daniel Leby cewa yana son komawa inda zai lashe kofi sakamakon cika shekara 27 a duniya amma ba tare da lashe wani babban kofi ba a wasannin da yakeyi na kungiyoyi.

Sai dai a kwanakin baya, a wata hira da yayi da manema labarai, shugaban na Tottenham Daniel Leby ya ce Harry Kane babban dan wasa ne kuma yana fatan zai iya janyo hankalinsa domin ya ci gaba da bugawa Tottenham wasa kuma zai zauna dashi bayan an kammala buga wasannin nahiyar turai na Euro 2020 da kasar Italy ta doke Ingila a wasan karshe a birnin London a ranar Lahadin satin daya wuce.

#hausaleadership

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button