Labarai

Furucin Bulama Akan Malamai Kuskure Ne

DAGA Datti Assalafiy
Bulama mai zane ‘dan jarida ne da yake zanen barkwanci ana sakawa a jaridu, Bulama ya yiwa Malaman addinin Musulunci barazana cewa idan ba su fito sunyi magana akan ‘yar gidan Sarkin Bichi da tayi shigar banza ba, to zaiyi zanen barkwanci mai kama da na batanci a kan Malamai

Hakika wannan maganar da Bulama yayi kuskure ne ko da ya fadi hakan da niyyar wasa ne, Malaman addinin Musulunci sun fi karfin a musu irin wannan barzanan, domin yana kama da rainin wayo da kuma cin fuska wa Malamai magada Annabawan Allah

Sannan a dayan bangare Bulama abin tausayi ne, saboda sana’ar zanen da yakeyi haramun ne a Musulunci, Manzon Allah (SAW) ya hana, da Nassin Hadisi duk abinda Bulama ya zana na surar mutum ko dabba Allah zai tuhumeshi ranar Hisabi, za’a kawo masa gabansa ace ya hura musu rai

To kun ga abinda Bulama ba zai iya ba kenan ya hurawa abinda ya zana rai, don haka makomarsa a ranar lahira abin tsoro ne idan bai tuba daga yin zane ba kafin lokaci ya kure masa

Muna yiwa Bulama fatan alheri, lallai ka canza sana’a, idan kuma ba haka ba to ka kiyayi shiga hurumin Malamai, ka tsaya iya kan ‘yan siyasa

Zai yi wahala a samu kirista mai zanen barkwanci irin na Bulama yayi barazanan yiwa Malamin addininsa na kirista zanen barkwanci ko na batanci, saboda suna girmama Malaman addininsu ko da basa kan ra’ayi daya, ya kamata Musulmi su kasance masu girmama Malamai da ganin kimarsu da darajarsu

Allah Ka kara mana shiriya, Ka kare mana mutuncin Malamai Magada Annabawan Allah Amin

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: