Addini

FURSUNONI SUNYI KUKAN RABUWA DA SHEIKH IDRIS DUTSEN TANSHI

FURSUNONI SUNYI KUKAN RABUWA DA MALAM

Daga Datti Assalafy

Lokacin da mushrikai da matsafan Bauchi suka yi sanadin shigar Malam Idris Abdul-Aziz Jami’ar Annabi Yusuf wato gidan yari, lokacin da Malam zai fita daga gidan yarin fursunoni sukayi ta kuka don basa son rabuwa dashi

 

Bayan Malam ya karantar da fursunoni a gidan yarin, ya dauki nauyin majinyata har da wanda ake masa chemotherapy na cutar kansa

 

Sannan Malam ya ‘yanta fursunonin da aka dauresu saboda sun kasa biyan kudin tarar da Kotu ta musu, ya biya musu kudin daga aljihunsa suka fita daga gidan yari

 

Dama mun fada muku, indai don Allah ne wannan daurin da aka yiwa Malam Idris alheri ne a gareshi da kuma karin daukakar daraja, gashi nan mun gani

 

Wannan shine banbancin Malamin Allah da Malaman bidi’ah mushrikai ‘yan damfara

 

Yaa Allah Ka kara wa Malam daraja, Ka tsareshi daga dukkan sharri na waliyyan shaidan a doron Kasa