Labarai

Fulani Makiyaya Na Yawo Bindiga Ne Domin Kare Kansu, Cewar Gwamna Bala Mohammed

A safiyar jiya Juma’a cikin hirar sa da Channels Tv cikin shirin su na Sunrise.

Gwamnan yace jawabin nasa “ishara ce kawai kan irin halin da Fulani suka tsinci kansu a ciki a halin yanzu domin nuna muku irin halin da suke ciki da irin abubuwan da ake musu saboda ana musu kallon da jami’in kalmar yan ta’adda,

“Gwamnan yace yanzu Fulani kullum zaluntar su ake yi, saboda ana musu kallon tsagera, kuma duk inda suka je, farautarsu ake yi. Ba a kudu maso yamma kadai ba ko kudu maso gabas kadai ba, har a Arewa saboda ana kwace musu dukiyarsu Shanu.”

Sannan “Wani lokacin kuma a cin tarar su saboda kawai shanun su sun shiga gonar wani.”

“Saboda haka Fulani ba su da wata mafita illa su kare kansu.”

Gwamnan ya ce akwai bukatar a yi musu adalci da samar da yanayin da zai basu tsaro yanda za’a taimaka wajen tsare su da shanun su daga farmakin ta’addanci. Yadda za a ke bambance nagari ciki da masu matsala.

A yi adalci ga kowa shine zai wanzar da zaman lafiya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: