Labarai

FRSC ta bukaci a riƙa amfani da shari’ar Muslunci wajen hukunta masu karya dokokin tuƙi 

FRSC ta bukaci a riƙa amfani da shari’ar Muslunci wajen hukunta masu karya dokokin tuƙi

Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa, FRSC, reshen jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi ya nemi da a fara amfani da tsarin shari’ar Musulunci don hukunta masu karya dokokin tuƙi domin dakile yawan afkuwar haɗurra tituna a kasar nan.

Ya yi wannan kiran ne a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa a yau Alhamis a Bauchi.

A cewarsa, dokokin da a ke amfani da su a kan hadurran tituna ba su da tsauri, don haka akwai bukatar shigar da dokar Shari’ar Musulunci a cikin dokokin tuƙi.

Abdullahi ya ce matakin zai sanya ladabtarwa, da karfafa mutunta dokokin tuƙi da kuma inganta yanayin tsaro a tsakanin masu ababen hawa.

Ya ce hakan zai kuma dakile yawaitar munanan haɗurra da ke faruwa a kan hanyoyi da kuma tukin ganganci.

“Mu gabatar da Shari’ar Musulunci a cikin shari’ar hadurran mota kuma mutane za su farka. Mutanenmu na da sakaci sosai, kuma masu abin hawa ba sa damuwa su rika duba su ababe hawan su.

“Idan ba mu gabatar da Dokar Shari’a Musulunci ba, yawancin masu amfani da hanya, musamman a wannan yanki ba za su hankalta ba.