Labarai

(FMARD) Ina Wanda Suka Cike Tsarin Tallafin Noma Ga Sako

Duk Wanda Ya San Ya Cika Tsarin FMARD, Kuma Ba Shi Da Asusun Ajiya Na Banki, Ya Gaggauta Budewa
…Sun bada tsawon kwanaki bíyar ga duk wanda ba shi da asusun ajiya da ya gaggauta budewa

Daga Comr Abba Sani Pantami

Gwamnatin Tarayya ta amince da tallafawa kananan manoma karkashin tsarin FMARD da kudaden da zasu sayi wadataccen kayayyakin noma a kason farko First Batch.

Tun tuni NIBSS ta tantance BVN din wa yanda zasu ci moriyar tsarin, za’a turo musu kudaden zuwa asusunsu na Bankuna.

Amma akwai mutane da dama da aka tantance wa yanda basu da Asusun banki a BVN din su, wannan dalilin yasa Hukumar take ta turawa duk wa yanda basu da Asusun banki Message da su gaggauta budewa kafun 7 ga Wannan watan, wanda yanzu haka suaran kwanaki Biyar su rufe.

Sunso su fara bada Kudaden cikin wannan makon, saboda tsaikon marassa asusun bankuna yasa Suka dage sai mako na gaba.

Tambaya: Yaushe manoma suka nemi tallafi a cikin tsarin FMARD?

Amsa: Tun shekarar da ta gabata Gwamnatin Nijeriya ta fitar da tsarin tallafawa kananan manoma a karkashin hukumar bada agajin noma ta FMARD.

Bayan kaddamar da tsarin a shekarar da ta gabata Gwamnatin Nijeriya ta wakilta tsoffin Ma’aikatan N-Power, inda suka dinga cikawa masu neman shiga tsarin bayansu a dukkannin jihohin Nijeriya, tare da gwajin gonakin mutane.

Miliyoyin kananan manoma ne suka samu damar neman tallafin.

Muna fatan ‘yan uwanmu ‘yan Arewa zasu fi kowa amfana.

Bayan an bawa First Batch akwai Second Batch InshaAllah kamar yadda suka fada.

Rubutawa✍🏻✍🏻✍🏻
Comr Abba Sani Pantami
National Chairman Of “Arewa Media Writers Association”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: