Kannywood

Fim: Kayi Nayi Ya Hada Kudi Kimanin Naira Miliyan 4 Da Dubu 667 A Cinema 1

Fim din KAYI NAYI ya haɗa kuɗi Naira Dubu Ɗari Shida da Hamsin da Huɗu (₦654,000) a ranakun makon sa na biyu. Inda yanzu yake da jimilar kuɗi (₦4,667,000).

Bisa al’ada ta sinima idan fim yayi irin wannan tashin gwauron zabi na kasuwa to idan aka shiga satin sa na biyu ragargazowa ƙasa kasuwancin sa yake, akan KAYI NAYI ba haka lamarin ya kasan ce ba, fim din ya rike wuta (trending) haɗa kuɗi 654k a Weekend din sati na biyu bakaramin kokari yayi ba. Wannan entire collections din wani fim dinne ma.

Abu na biyu da masu karatu mukeso su fahinta shine, wannan tarin kudi a iya cinema daya rak ya hadashi, wanda bamaji a wannan yanayi da ake ciki a kwai wani film da zai iya haka a duk faɗin Nigeria. Misali idan ka dauki fim din dayake na biyu akan chart a wannan karshen mako MAMBA’S DIAMOND, film ne na NOLLYWOOD wanda dama finafinan HOLLYWOOD da NOLLYWOOD ne suke mamaye gurbin na ɗaya zuwa na biyar kusan koda yaushe. Zamu ga ya haɗa kuɗi ₦7,171,800 a ranakun ƙarshen makon sa na biyu. Muna yawan cin karo da comments na masu karatu cewa fim din kudu yana haɗa millions of Naira amma na Kannywood milyan uku sai muyi ta zuzutawa. Ga lisafin MAMBA’S DIAMOND ya haɗa Milyan bakwai din can a sinimu 53 wanda idan ka dauki Average na kudin daya kawo a kowacce sinima zaku ga baifi ₦135k ya kawo ba kenan, a yayin da KAYI NAYI ya haɗa ₦654k. Wannan tasa muke cewa da finafinan Kannywood zasu samu yawan sinimun nan da duk sati film din Kannywood ne zasu dinga mamaye jadawalin. Idan kun lura daga shekara hudu zuwa iyanzu cinikayyar finafinan Kannywood kara haɓaka take da wannan zamu iya hasashen nan bada jimawa ba a sinima daya milyan goma zata dinga futa.

Zuwa karshen makon nan fim din KAYI NAYI zai dare karagar BIGGEST KANNYWOOD GROSSERS karagar da fim din MATI A ZAZZAU ya dare har tsawon wata goma sha shida.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: