Fim din ‘Kanwar Dubarudu’ fim ne sabo wanda kamfani mai shadda ya shirya shi. za’a haska wannan fim a Cinema ranar 30/6/2017 akan kudin shiga naira dubu daya kacal. wanda zai fito kasuwa a washe garin da aka haska shi a cinema, za’a sayar da shi akan kudi naira 100 kacal.
Jama’a masu tarin yawa sun kosa wannan fim ya fito kasuwa. sabida labarine wanda aka gina shi akan nishantarwa, mai tattare da fadakarwa. manyan mutane masu sukuni sune suka fi nuna kagara fim din ya fito kasuwa.
A dalilin farin jinin da fim din ya yine yasa Sarki Ali Nuhu ya kara samin farin jini a idanun masu kallo. domin ya taka rawar gani a fim din. ya kayatar fiye da yanda akayi zato.
Sulaiman Bosho da Rahma Sadau suma sun nuna namijin kokari acikin fim din ‘Kanwar Dubarudu’. Domin sunyi duk abinda darakta ya umarce su suyi. Rahma Sadau ta burge sosai acikin fim din, domin tayi abinda ba’a zata ba, amatsayinta na Pyranka. (Sarauniyar Kwalliya).
Add Comment