Kannywood

Kannywood: Fati Mohammad Ta Zama Daraktar Gidauniyar Atiku Abubakar

Fati Mohammad Ta Zama Daraktar Gidauniyar Atiku Abubakar

Tsohuwar jarumar finafinan Hausa, Hajiya Fati Mohammad ta zama daraktar harkokin mata na Gidauniyar Atiku, wato ‘Atiku Care Foundation’ (ACF) reshen jihar Kaduna.

Fati wadda ‘yar asalin jihar Adamawa ce, tana daya daga cikin jaruman fim din Hausa da suka shahara a shekarun baya, inda yanzu haka take zama a jihar Kaduna.

 

Fati wadda ta fito a finafinai irin su Sangaya, Zarge, Marainiya da sauransu, jakada ce a kungiyar UNICEF. Sannan kuma an ba ta matsayin ne duba da yadda ta kasance mai taimakwa marasa galihu.

Takardar da ke dauke da sanarwar matsayin da aka baiwa tsohuwar jarumar, na dauke ne da sa hannun shugaban Gidauniyar Ta Atiku reshen Kaduna, Ibrahim Dahiru Danfulani.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.