Labarai

Fatalwar’ Adolf Hitler ta bayyana a mahaifarsa da ke Austria

Adolf Hitler ya jagoranci Jamus daga 1933 zuwa 1945
Wani matashi mai suna Herald Hitler wanda aka ce yana kama da tsohon shugaban gwamnatin Nazi na Jamus, Adolf Hitler, ya bayyana a kasar Austria.
Herald Hitler wanda shekarunsa ba su wuce 25 zuwa 30 ba, ya bayyana ne a wata mashaya da ke garin Braunau amm Inn wanda mahaifar Adolf Hitler ce.
Mazauna garin sun ce gashin bakin matashin wanda faffada ne kuma a cunkushe a kofofin hanci, ba maraba da na Hitler na asali.
Sannan kuma irin yadda yake gyaran gashin kansa ya yi kama da na shugaban gwamnatin Nazi.
Shi dai Adolf Hitler ya na gicciyar da gashin kanasa zuwa gefen hagu, ya kuma bar wata ‘yar tsaga da ta yi wa gashin na bangarorin biyu iyaka.
Har wa yau, Herald Hitler na sanye da tufafi irin wanda jagoran na Nazi yake sanyawa.
An kuma ce matashin na dauke da wani hotonsa wanda aka dauka a gaban gidan da aka haifi Adolf Hitler.
Yana da yankakken gashin baki mai kauriHakkin mallakar hotoPA
Image captionYadda Hitler yake gyaran gashi
Rahotanni sun ce wuri na karshe da aka ce an ga matashin, shi ne wani shagon sayar da littafi, yana ta faman neman litattafan da suka yi tsokaci kan yakin duniya na biyu.
Yanzu haka dai ra’ayi ya banbanta kan wane ne hakikanin shi wannan mutumi.
Yayin da wasu ke masa kallon fatalwar tsohon jagoran jam’iyyar Nazi ta Jamus wato Adolf Hitler, wasu ko na ganin Tagwansa.
Amma da dama na da ra’ayin cewa mutumin mai ra’ayin jam’iyyar Nazi ne da ke son tayar da zaune tsaye.
Tuni dai hukumomin kasar na Austria suka baza komarsu wajen neman wannan mutum da wasu ke ganin fatalwar Adolf Hitler ce.
Da man dai hukumomin Austriyar sun kwace gidan da aka haifi Hitler a watan Yulin 2016 bisa tsoron fadawa hannun burbushin ‘yan jam’iyyar ta Nazi.
An haife shi ne a tsohuwar kasar Austria-Hungary
Image captionGidan da aka haifi Hitler a Braunau amm Inn
A shekarar 1889 ne aka Haifi Adolf Hitler, a garin na Braunau am Inn wani yanki na tsohuwar kasar Austria da Hungary.
A 1938 ne kuma Jamus, karkashin gwamnatin Nazi wadda Adolf Hitlan ya jagoranta, ta mamaye Austria,ta kuma hade ta a cikin kasarta.
Shi dai Adolf Hitler ya jagoranci kasar Jamus daga 1933 zuwa 194.
Sai dai masana tarihi sun ce, Hitler ya yi wa al’ummomi da dama gashin kuma musamman lokacin yakin duniya na biyu.