Raayi

Farfesa Gwarzo Sarkin Yaki Da Jahilci Na Afrika

Daga Sani Tahir Kano,
Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, shi ne ya Samar da Gidauniyar( AAG foundation)

Gidauniyar Dakta Musa Abdullahi Sufi. shi ne Babban mai ba da shawara wajen Tafiyar da Gidauniyar Farfesa Adamu Abubakar fitaccen dan Gwagwarmaya a fagen ilimi a Nahiyar Afirka. Mutum ne da ya kasance mai fafutukar ganin al’umma sun samu Kyakkyawar rayuwa musamman ta bangaren ilimi da lafiya. Tsayayye ne kuma jajirtaccen namiji mai tausayin na kasa da shi, kullum kokarinsa ya ga ya tallafawa matasa da marasa hali.

Dubban matasa sun yi Ilimi ta dalilinsa, wasu dubbai sun yi ilimi a aljihunsa. Kokarinsa da farar zuciyarsa ta sanya ya zama Abin koyi daga cikin wadanda suka yi karatu a jami’o’in kudi a nahiyar Afirka, da Tarayyar Nigeria.

Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, Mamallakin Jami’ar Maryam Abacha Amurka ,(MAAUN) dake Nijer, Sardaunan Hausawan Turai, Sarkin Yaki da jahilci na Afirka, wanda a wannan yanki na mu na Afirka ba za a manta da shi ba domin ya Gina dan’Adam ta hanyar samar da jami’o’i a kasashen Nigeria, Niger, Ghana, Togo, wanda an tabbatar da duk fadin Afirka babu wata jami’a mai zaman kanta sauki kamar ta dan masanin Gwarzo ba, haka kuma har a kasar France da England.

A cikin wannan Gidauniyar ta Farfesa Gwarzo sun fi mayar da Hankalinsu wajen kula da inganta harkar ilimi, wanda suka dauki ilimi da matukar muhimmancin Gaske, wannan dalilin ya sanya ba dare ba rana suke bayar da tallafi a harkar neman ilimi domin karfafa wa daliban ilimi gwiwa don su ma, su samu madogara, madogarar da suma za su tallafa wa sauran dalibai na baya. Ana ba wa da yawa daga cikin Talakawa wadanda ba za su iya daukar nauyin kansu gurbi a Jami’ar (MAAUN) ta karkashin Gidauniyar Adamu Abubakar Gwarzo kyauta.

Bai Tsaya iya nan ba sai da ya tsallaka Jami’o’in Gwamnatin Tarayya da Jihohi. Jami’ar Bayero dake Kano (Buk), Jami’ar ta samu tallafin Babbar Mota mai daukar sama da mutum 60, da kuma kujeru na miliyoyin kudi Wwanda aka bayar a saka a (Senate Building) da sauran dalibai. Haka ita ma Jami’ar Tarayya ta Dutsenma, (Fudma) ta rabauta da Mota har guda Biyu, wanda su ma domin amfanin daliban Jami’ar wajen rage mu su dawainiya wajen tafiye-tafiye don gudanar da bincike, dayar kuma motar daukar mara lafiya, wanda a bawa Asibitin da yake cikin jami’ar ta Dutsenma, da iittattafai na miliyoyin Naira duk domin amfanin dalibai Kaduna Polytechnic ta samu kyautar Mota mai daukar mutum 60,Jami’ar Yusuf maitama Sule Unibersity, mallakin jihar Kano,itama ta samu tallafin kyautar mota don inganta harkokin koyo da koyarwa a cikin Jami’ar.

Bai tsaya iya kacin jami’o’i ba, sai da ya kalli bangaren firamare da sakandare inda aka daga darajar makarantu da dama a karkashin gidauniyarsa kama daga kananan makarantu zuwa manya a kokarinsa na ciyar da ilimi gaba a wannan yanki na mu na Arewa da kasa. Ya gina Ajujuwa wadanda suka lashe miliyoyin Naira a Karamar Hukumar Gwarzo, wasu an kammala aikinsu, wasu a halin yanzu ana tsakiyar aikin, wannan gidauniyar ta kan dauki nauyin daliban da Allah ya sa suka zama masu hazaka tun daga matakin firamare har zuwa Jami’a, wasu sun kammala har sun fara Aiki, wannan aka sanyawa wata makaranta sunansa da aka Ggna, wannan kadan ne a kan abin da ya shafi harkar ilimi.

Harkar kiwon lafiya nan ma dai wannan Gidauniyar ta na yin iya kokarin Abin da Allah ya nufa za’a yi, akwai dalibai sama da Mutum 200 wadanda suke kara kwarewa a harkar lafiya daga Masu, Digiri zuwa matakin PhD, wadanda sarkin yaki da jahilci na Afirka yake biya wa kudin Makarantarsu, wanda ba ‘ya’yan kowa ba ne.

Babban burin gidauniyar idan su ma sun kammala su tallafawa wadansu.samun irin Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ba karamin cigaba ne a Arewa da kasa baki daya.

Wasu daga cikin Makarantu da na kawo sunansu, sai da aka basu gudummawar littafai na manyan kudadd domin amfanin dalibai masu karatun Lafiya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: