Uncategorized

Faransa za ta kara da Jamus a wasan daf da karshe

Tawagar kwallon kafa ta Faransa ta kai wasan daf da karshe a gasar cin kofin nahiyar Turai, bayan da ta doke Iceland da ci 5-2 a karawar da suka yi a ranar Lahadi.

Faransa ta fara cin kwallo ta hannun Olivier Giroud, sai Paul Pogba ya kara ta biyu, Dimitri Payet ne ya ci ta uku, sannan Antoine Griezman ya ci ta hudu daf da za a je hutun rabin loaci.
Bayan da aka dawo daga hutu ne Iceland ta ci kwallo ta hannun Kolbeinn Sigthorsson da kuma wadda Birkir Bjarnason ya ci daf da za a tashi daga karawar, kafin nan Faransa ta ci kwallo na biyar ta hannun Olivier Giroud.
I zuwa yanzu Antoine Griezman ne ke kan gaba a matsayin wanda ya fi cin kwwallaye a gasar, Inda ya zura hudu a raga a wasannin.
Da wannan sakamakon Faransa mai masaukin baki, za ta kara da Jamus a wasan daf da karshe a ranar Alhamis a Marseille.
Jamus ta kai wasan daf da karshe ne a gasar, bayan da ta fitar da Italy a bugun fenariti da ci 6-5, bayan da suka tashi wasa kunnen doki 1-1.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.