Labarai

An fara Gyare Gyaren Dawowar Shugaba Buhari A Villa

YANZU HAKA AN FARA GYARE-GYARE DA KINTSE-KINTSE DAWOWAR SHUGABAN KASA MUHAMMAD BUHARI A VILLA.

Daga Shafin Jiridar Damukaradiyya

Ma’aikatan fadar Shugaban kasa Muhammad Buhari sun kasa zaune sun kasa tsaye da aikace-aikace da shirye-shiryen dawowar Shugaban kasa Muhammad Buhari a Villa.

 

Wani na kusa da Shugaban kasa Muhammad Buhari Wanda ya bukacin a sakaya sunan shi ya bayyana wa wakilin mu Shuaibu Abdullahi cewa zuwa yanzu an kammala dukkan shirye-shirye Buhari kawai ake jira.

Jaridar Dimokaradiyya ta ruwaito cewar tun jiya wasu daga cikin masu yima Buhari da Uwargidan shi hidima sun dawo nan gida Najeriya saboda shirye shiryen dawowar su.

A wani rahoto na daban kuma ana saka ran dawowar Shugaban kasa Muhammad Buhari a cikin wanna makon da muke a ciki.

Idan baku manta ba yau Shugaban kasa Muhammad Buhari ya kwashe a kalla kwanaki tamanin da bakwai 87 a kasar London yana zaman Jinya.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.