Addini

Falalar Goman Farko Na Watan Zul Hijja

A yau Laraba daya ga watan Musulunci mai Alfarma wato watan Zul Hijja na shekara ta 1441. daidai da 22nd July,2020

Ga wasu daga cikin falalar wannan wata da kuma abubuwan da ake bukatar Musulmi mu yi don samun ribar wannan watan:

* Allah yayi rantsuwa da wannan ranaku a cikin alqur’ani maigirma

‎الفجر وليال عشر

Jamhurun malamai sun fassara wannan ranaku da goman farko na Zul Hijjah Alhafiz Ibn Kasir cikin tafsirinsa yace “wannan shine magana mafi inganci”

* Idan watan Zul Hijjah ya tsaya babu kyau ga wanda keda niyan layya yayi aski ko yankan faratu annabi ya hani da hakan. Duba cikin sahihu muslim1977

* Jigajigan rukunan musulunci ana samunsu ne cikin Zul Hijjah
~Tauhidi yadda alhazai suke talbiya
~Sallah ta idul adha
~Sadaka tayadda wanda yayi tamattu’i ko kirani zai hadaya a rabawa miskinai da mabukata
~Aikin hajji da wannan babu wani watan da ake samun wannan aiyukan gaba ki daya sai cikin Zul Hijjah.
Duba cikin fathul-bari juzu’i na 2 shafi na 460
* Aikin hajji na kankama ne cikin goman farko tun daga ranar takwas zuwa ranar sha uku ga wata
* Ranar Allah yafi yanta bayi daga wuta cikin goman farko ne wato ranar Arfa.
* Cikin goman farko Allah ya umarci alhazai su ambace shi a Masha’arur-haram wato ranar goma ga wata

* Azumin ranar Arfa na cikin goman farko ne wanda ake ranar tar ga wata ga wanda keda ikon yi kuma bai samu zuwa aikin hajji ba Azumin na kankare zunubai.

* Cikin goman farko ake kabarbari sabanin sauran watanni kana ma الله اكب الله اكبر لا اله الا الله الله اكبر الله اكبر و لله الحمد
Abu Huraira da Abdullahi Ibn Umar suna fita kasuwa cikin goman farko suna kabarbari mutane suna kabbara da kabarbarinsu. duba cikin fathul bari juzu’i na 1 shafi na 458 cikin hadisin Abdullahi bn Umar yace Manzon Allah s.a.w yace
‎ما من ايام اعظم عند الله و لا احب اليه من العمل فيهن من العشر فأكثيرو فيهن من التهليل واتكبير واتحميد
Ma’ana Manzon Allah s.a.w yace Babu wata rana da aiki na gari yafi daukaka da soyuwa ga Allah fiye da kwanaki goma na farkon Zul hijjah saboda haka ku yawaita wadannan kalmomin
La’ilaha illalah Allahu akbar walillahil hamd

* Hafsa bint Umar radiyallahu anha tace
‎اربع لم يكن يدعهن انبي صل الله عليه وسلام صيام عشوراء والعشر و ثل ثة ايام من كل شهر والركعتين قبل الغداة
Ma’ana abubuwa hudu Manzon Allah s.a.w baya taba barinsu
~Azumin Ashura goma ga watan Muharrah
~Azumin goman farko na Zul Hijjah
~Azumin kwanaki uku a kowane wata
~Raka’a biyu kafin sallar asubahi
Musnad Imamu Ahmad Ibn Hambal hadisi na 25,920

* Cikin wannan wata ne aka cika mana addini wato ranar Arfa kamar yanda Buhari ya ruwaito 4606

* Fiyayyen addua itace adduar ranar Arfa tara ga watan Zul Hijjah

* Watan Zul Hijjah shine cikamakin watanni sanannu wanda Allah yace الحج اشهر معلومات

* Kuma cikin watan Zul Hijja ne Allah ke alfahari da bayinsa da suka halarci Arafa
Allah yasa mu dace Amin

Sen Ibrahim Shekarau CON,PEN
(Sardaunan Kano)

Haarun

Haruna Lawan Usman is a certified Animal Health and Production Technologist, with more than 4 years experience in Animal Health and Production Technology.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: