Addini Nasiha

FA’IDODI SHA BIYAR(15) TATTARE DA WATAN RAMADAAN DA KUMA AZUMI

 

1- Bautar Allah, wato yin azumin bautar Allah ne, karanta Suurah ta 2:183. Mafi girman fa’idah ga mumini kuwa shi ne bauta ma Allah.

2-Babu wani wata da Allaah Madaukaki Ya kebe da saukar da mafificin littafinSA  in ba Ramadaan ba(Q2:185)

3-Yawan karanta da kuma tilawar al-Qur’aani maigirma. Babu wani wata da  a ke karanta al-Qur’aani maigirma da yawa irin watan Ramadaan.

4-Samun dare wanda ya fi wata dubu wajen falala da al-Khairi wato daren Laylatul Qadri, al-Qur’aani 97:3 (wato wanda ya dace da yin Ibaadah cikin wannan dare, tamkar ya yi ibadar shekara tamanin (80) ne!

5-Kukkulle kofofin Wuta da kuma bubbude kofofin al-Jannah, wato ishara ga yawaitar Rahmah da kuma hanyoyin samunta da kuma tsukewar kofofin Azaba

6-Yawaitar tsayuwar dare wadda ba’a samun haka in ba a watan Ramadaan ba.

7-An fi samun yawan ciyar da dukiya kan hanyoyi na alkhairi a Ramadaan sama da sauran watanni.

8-Majalisai na bayani da kuma fassara al-Qur’aani

maigirma sun fi yawaita a Ramadaan sama da ragowar watanni.

9-A dalilin watan Ramadaan, musulmin Duniya gaba daya kan samu wani yanayi na karin hakuri ga barin ci da sha da kuma dangogi na sha’awa.

10- Ibaadar I’tikaafi-wadda Ibaada ce mai matukar romo da tsoka- a watan Ramadaan ne tafi kankama

11-A kwai wata kofa mai suna ar-Rayyaan masu azumi kadai ke shiga al-Jannah ta cikinta(Allaah KA sa muna cikinsu)- Hadiithin Bukhaary da Muslim. Ibaadar da ke ba mutum cancantar shiga al-Jannah ta wannan kofa ai a watan Ramadaan tafi bayyana kuma wadda take daya daga cikin shika-shikan Musulunci.

12- Yana daga cikin falalar watan Ramadaan cewa yin ‘Umrah a Ramadaan na daidai da Hajji tare da Manzon Allaah- sallal Laahu ‘alayhi wa sallama.

وعنِ ابنِ عباسٍ، رضي اللَّه عنهُما، أنَّ النَّبيَّ ﷺ قَالَ: عُمرَةٌ في رمَضَانَ تَعدِلُ حجة أَوْ حَجَّةً مَعِي متفقٌ عليهِ

13-Bashin bakin mai azumi a wajen Allaah ya fi al-Miski kamshi(Bukhaary da Muslim). Watan Ramadaan shi ne kan gaba wajen samar wa  Muminai wannan garabasa.

14-Sanya miyagun aljannu da ibilisai cikin sarka da dakawrori da sarkoki a daren farko na Ramadaan

(Ibnu Khuzaimah da Tirmidhy da Nasa’iy da Ibnu maajah kuma sahiihi ne)

15-Tace jini da kuma habaka lafiya da ke tattare da Azumi.

Da sauransu domin ire-iren wadannan darajoji da falala na Ramadaan na da yawa.

ALLAAH, KA NUNA MANA RAMADAAN KUMA KA BAMU IKON AZUMTARSA YANDA YA DACE.

_*Shaykh Muhammad Bin Uthman*_

About the author

Haarun

Co-founder Arewablog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.