Labarai

Fadar shugaban Najeriya ta tabbatar da cewa za a rusa kamfanin mai na NNPC

Fadar shugaban ƙasar tace rushe kamfanin na cikin sauye-sauyen da za a iya wa fannin man fetur a Nijeriya karkashin sabuwar dokar inganta harkokin man fetur.

Sai dai gwamnatin ta ce za a maye gurbin kamfanin na NNPC da wani mai zaman kansa.

Fadar shugaban ƙasar tace wannan na daga cikin ayukkan da aka dorawa kwamitin share fage kan aiwatar da dokar da Shugaban Muhammadu Buhari ya sanar da kafawa a dazu yayin taron majalisar ministoci na mako-mako.

Ministan albarkatun man fetur Timipreye Silver ne zai jagoranci wannan kwamitin da zai lura da yadda za’a rusa kamfanin cikin nasara.

Zamu jira sharhin masana kan wannan yunkuri fage ne dake bukatar masana su fayyace shi. Dalla-dalla.

Masu karatu kuma kuna iya tofa albarkacin bakin ku.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: