An jawo hankalin fadar shugaban kasa ga rahotanni cewa shugaba Muhammadu Buhari ya ki sauraron gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano a lokacin bikin murnar sallar Eid-el-Kabir da aka yi a kwanakin baya, wanda shugaban ya yi a garinsa Daura da ke jihar Katsina.
Wannan rahotanni ta kasance daga masu neman ba ta siyasar gwamnan ne, wadanda suke so su yi amfani da al’amarin don cimma wani buri.
Mai magana da yawun shugaba Muhammadu Buhari, Femi Adesina ya ce: ‘’Shugaban kasar ya karbi gwamna Ganduje tare da wasu gwamnoni makonni da suka wuce a Landan, kuma gwamnan ya yi maraba da shugaban
kasar, tare da sauran mutane a lokacin da shugaban ya dawo kasar a ranar 19 ga Agusta. Me yasa shugaba Buhari zai ki sauraron sa kamar yadda aka ruwaito, musamman a kan kafofin watsa labarai?”
Mikiya
Add Comment