MAI CIKI
Assalamu Alaikum WarahmatullAllah Wabarakatuhu.
Sau da yawa wasu mazan sukan yi wani irin babban kuskure. Wannan kuskuren kuwa shi ne kauracewa matan su yayin da suka sami ciki. Wani mijin da zarar matarsa ta dauki ciki shi kenan sai ya daina cin abincin ta, ya daina yi mata magana, kai wani ma ko rabarta baya kara yi. Habba! Wannan irin gidadanci har ina? Kaga,, a matsayin ka na miji ya kamata ka san cewa hakki ne a wuyarka na ka tabbata matar ka tana cikin farin ciki da walwala, a lokacin da ta ke da ciki kuma ya kamata kasan cewa tana bukatar kula na musamman daga gare ka. Mazajen da suka san me ake nufi da nunawa mace so, da zarar T dauki ciki, to shi fa shi kenan zaman hira a waje ya kare kenan (idan ma fa yana yi din kenan). Meeting ma sai ya zama dole za shi. Hatta bandaki in zata shiga shi zai kaita kuma ya dawo da ita. Yayin da suka zauna kuma sai yayi ta bata labaran ban dariya da Nishadi. Irin hakan ne ke sa shi kan shi yaron ko yarinyar tun yana cikin ciki sai kaji yana cewa: “ah Baba na yana son mama ta sosai, lallai na nima dole in nuna musu soyayya sosai idan na fito”. Idan kuwa matar ta zo Haihuwa, shi zai dinga karfafa mata guiwa yana yabon ta bisa irin kokarin da kuma dawainiyar da ta ke yi na kula mai da abubuwan sa da dai makamantan hakan. Zaka ji yana mai cewa : daure dai Masoyiyata, nasan zaki iya, na yarda da ke, nasan cewa kina iya bakin kokarin ki amma dai ki kara dagewa. Da irin haka sai kaga wata mace kafin kace kwabo, cikin yardar Allah har ta sauka lami lafiya. Amma shi kuwa miji Bagidaje, idan ma Ya dawo gidan sai dai ya zauna yayi shiru kamar an yi masa mutuwa, ba uhum ba um um. Irin haka ne sai kaji shi kan shi dan dake cikin yana ayyanawa a ransa : “Kai ku tsaya, anya ma gidan nan lafiya kuwa, naga kamar ma fa basa murna da zuwa na ne. Lallai in na fito dole su gane”. In kuwa matar ta zo Haihuwa, kuma aka ci Sa’a yana wurin sai dai kaji yana cewa : “kai! Amma wannan anyi ja’ira, yanzu da ci ne ta san yadda ake yi amma tun dazu ta kasa Haihuwa, ja’ira dama ko wurin girki haka ta ke da Ragwanta! Habba mana menene haka Fisabilillah? Kai fa mijinta ne, kuma kar ka manta fa ba kofin ruwa ta sha fa ta sami wannan cikin ba. Lallai ya kamata masu irin wannan dabi’a da su daina bata da kyau kuma bata dace da musulmi ba. Allah Ya Shiryar da mu hanya Madaidaiciya Ameen.
Haiman Khan Raees @HaimanRaees
Add Comment