Facebook Zai Fara Fallasa Labaran Karya

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Kamfanin Facebook ya sanar da sabbin matakai da za su taimaka wajen yaki da labaran kanzon kurege a shafinsa na sada zumunta.

A wata sanarwa, kamfanin ya ce yanzu zai rika nuna bayanan da ba na gaskiya ba, wanda masu bin diddigi suka tabbatar da hakan, a shafukan Facebook da Instagram.

Kwanan nan ne Facebook ya fadada shirinsa na bin diddigi zuwa kasashe 10 a kudu da hamadar sahara: Habasha da Zambia da Somaliya da Burkina Faso da Uganda da Tanzania da Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Ivory Coast da Guinea da Ghana.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 23

Shugaban sashen manufofi a Afirka na kamfanin, Kojo Boakye ya ce za a kaddamar da shirin ne ta hanyar amfani da abokan huldar kamfanin kamar su Africa Check da Pesa Check da Dubawa da France 24 da AFP Fact Check a kokarinsa na toshe hanyoyin da labaran karya ke bazuwa a shafin Facebook.

Ya ce “daukar matakai don hana labaran karya bazuwa a Facebook hakki ne da ya hau kanmu kuma dole mu dauke shi da muhimmanci, mun san cewa labaran karya sun zama matsala, kuma wadannan su ne matakai masu muhimmanci da muka dauka don shawo kan matsalar.

Mun san cewa bin diddigin ba shi ne kawai mafita ba, amma hanya daya ce da muke sa ran za ta taimaka wajen inganta labaran da mutane ke gani a Facebook. Yayin da mun samu ci gaba, za mu ci gaba da zuba kudi don tabbatar da cewa Facebook ya kasance waje na samun wayewar kai amma ba waje na bazuwar labaran karya ba.”

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.