Labarai

Facebook da Whatsapp na bata tarbiyyar 'yan mata — Sultan

hugaban majalisar koli ta lamurran addinin Islama a Najeriya, ya gargadi yara musamman ‘yan mata da su guji daukar lokaci mai yawa kan shafukan sada zumunta na zamani domin yin hakan ka iya bata tarbiyarsu.

Da yake jawabi a wajen wata gasar musabakar Alkur’ani mai girma a birnin Sakkwato ranar Lahadi, Sultan Saad Abubakar, ya ce, “abin damuwa ne matuka” ganin irin yadda shafukan sada zumunta kamar su Facebook da Whatsapp da Instagram da 2go ke dauke wa yara hankali daga karatunsu.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ambato shi yana cewa ya kamata iyaye su rinka kula da yaransu.
”Irin yadda ‘yan mata ke bata mafi yawan lokutansu a kan shafukan sada zumunta abin damuwa ne kuma wannan yana da hadari ga al’ummarmu.
Yara mata su ne kashin bayan tarbiyya da kuma ci gaban al’ummarmu don haka idan suka kauce hanya, to dukkanin al’umma za ta shiga hadari domin su ne iyayenmu kuma masu yi wa yaranmu tarbiyya.”
Ya yi kira ga iyaye da su tabbatar da cewa ‘ya’yansu mata sun yi amfani da lokacinsu wajen yin abubuwa masu ma’ana da rayuwa, ciki har da karatun Alkur’ani, domin yin hakan ne zai sa su zamo iyaye na-gari”.
An dade an nuna damuwa kan illar shafukan sada zumunta ga tarbiyyar yara, musamman mata duk da irin farin jini da shafukan ke da su a tsakanin al’umma musamman matasa.
 
Ma’abota amfani da shafukan sada zumunta wadanda suke tattauna muhimman al’amura suna yawan korafi cewa, a kan samu ‘yara marasa tarbiyya’ su dinga zagin mutane kan wata mas’ala da ake tattaunawa a kanta, ba tare da la’akari da cewa mutum ya girme su ba.
“Al’amarin ba dadi sam, sai ka ga kanin bayanka ya zo shafinka ya dura maka zagi don kawai wani ra’ayinka da ka bayyana bai zo daidai da nasa ba,” in ji wani mai amfani da shafukan sada zumunta da ya bukaci a boye a sunansa.
Ita ma wata ma’abociyar amfani da shafukan sada zumuntar Safiyya Abbas, cewa ta yi, “Ai gaskiya abin ba dadi musamman yadda ‘yan mata ke baje kolin tsiyarsu a Instagram da wallafa hotuna masu nuna tsiraici da sauran su, dole kan iyaye su tashi tsaye.”

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.