Labarai

Etisalat Zai Janye Daga Nigeria

Akan Wane Dalili Zasu bar nigeria

Rahotanni daga Dubai na cewar kamfanin Etisalat ya ce zai janye samfurinsa daga Najeriya.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito cewar uwar kamfanin Etisalat dake birnin Abu Dhabi na hadaddiyar Daular Larabawa ya warware yarjejeniyar gudanarwa da ke tsakaninsa da reshensa na Najeriya tare da ba shi lokacin janye aikinsa.

Wannan matakin ya biyo bayan gazawar da kokarin hukumar kula da kamfanonin sadarwar Najeriya ta yi na ceto kamfanin daga durkushewa ta hanyar sake yarjejeniya kan bashin dala biliyan 1.2 da bankuna ke bin kamfanin.

A cikin watan Yuni ne a ka umurci kamfanin Etisalat, wanda ke da kashi 45 cikin 100 na jarin kamfanin na Najeriya, da ya mika hannun jarinsa na kamfanin zuwa ga wasu amintattu.

 

Shugaban uwar kamfanin Hatem Dowidar, ya ce dukkan masu hannayen jari na kamfanin Etisalat Nigeria da ke Hadaddiyar Daular Larabawa sun janye daga kamfanin.

Ya kara da cewar uwar kamfanin na ci gaba da tattaunawa da Etisalat Nigeria domin ba ta tallafi na fasaha.

Kazalika ya ce kamfanin Etisalat Nigeria zai iya ci gaba da yin amfani da sunan kamfanin har nan da sati uku kafin ya daina amfani da shi gaba daya.

 

SOUCE IN BBCHAUSA

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.