El`rufai Ya Tarwatsa Masu Garkuwa Da Mutane A Hanyar Kaduna Da Abuja


0 294

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Wannan Fa Jarumta Ce Gwamna El Rufa’i

Da ranar yau Laraba ne jami’an tsaro masu tsaron lafiyar gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i suka tarwatsa masu garkuwa da mutane da suka tare hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Gwamnan dai yana kan hanyarsa na dawowa daga Abuja sai ya samu ‘yan bindigan sun tare hanyar a daidai kauyen Alkiblu da misalin karfe 3:40pm.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 607

- Advertisement -

Jami’an tsaron gwamnan sun koresu a daidai lokacin ‘yan ta’addan suka shige daji.

Bayan an bude hanyar ne gwamnan ya bayar da umurnin a dauki wadanda suka sami rauni a kaisu asibiti mafi kusa.

Gwamnan ya yi alkawarin samar da dawwamammen zaman lafiya a hanyar.

Sanarwa Samuel Aruwan
Babban mai taimakawa gwamnan a bagaren labarai
3/04/2019.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.