Gwamna El-Rufai Ya Girgiza Abokan Adawarsa
Gwamna El-Rufai yau Litinin ya girgiza abokan adawarsa a lokacin da ya shiga Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa da Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu.
Gwamnan wanda yau ya shiga yakin neman zabe wadannan kananan hukumomin bayan ya gama ganawa da masu ruwa da tsaki na Kananan hukumomin Kaduna ta Kudu da ta Arewa inda ya bayyana musu irin ayyukan da gwamnatinsa ta yi a shekaru ukun nan.
Sarakuna da malaman addinai da shugabannin kungiyoyi a jawabansu a taron sun jinjina wa gwamnan musamman na irin kokarin da ya yi a harkar tsaro da fannin ilimi da kiwon lafiya da kuma samar da abubuwan more rayuwa.
Dubun dubatan maza da mata ne suka fito a lokacin da gwamnan ke zagaye suka tsare motarsa har suka tilasta masa sai da ya fito ta saman mota musamman a Tudun Wada, mazabar Sanata Shehu Sani har mutanen Kasuwan Barci suka ba shi kyautar mota a matsayin gudummuwarsu.
#Mikiya