Labarai

El-Rufai Ya Zargi Ganduje da Biyan Kungiyar Kwadago Kudi Domin Yin Zanga-Zanga A Jihar Kaduna

Daga Suleiman Abba (TBABA)
Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya zargi gwmanan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da biyan toshiyar baki ga kungiyar Kwadago ta kasa NLC don kawo cikas ga tattalin arzikin jihar Kaduna.

A farkon makon nan ne dai kungiyar kwadago ta tsayar da al’amura cak a jihar Kaduna biyo bayan korar ma’aikata da gwamna El-Rufai ya yi.

El-Rufai da Ganduje duk da suna Jam’iyya guda sai dai suna yawan samun sabani.

A wani Faifan Audio dake yawo a kafafen sadarwa na zamani mai dauke da sautin murya an jiyo El-Rufai na sukar Ganduje tare da zarginsa da biyan kudi ga yan kungiyar kwadagon domin gudanar da zanga zangar.

“Duk wannan abun da ke faruwa Ganduje ne ya biya su kudi, sun zo daga Kano. Yayin da suka je Kano, an biya su kudi sannan suka zo nan”, inji gwwmnan.

An dade dai ana ga maciji da Ganduje da El-Rufai tun bayan da Ganduje ya tsige babban Aminin El-Rufai, Malam Muhammadu Sanusi daga Sarautar Kano.

Sai dai har yanzu babu wani martani da gwamnatin jihar Kano ta mayar kan zargin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: