Labarai

EFCC Ta Sake Samun Dalar Amurka Miliyan 37.5 A Wajen Diezani

Hukumar Yaki Da Cin Hanci DA Rashawa Ta Nijeriya EFCC ta ce ta samu tsabar kudi wuri na gugan wuri har Naira biyan 11.5 da ta ke zargin mallakar tsohuwar ministar man fetur din kasar ce, Madam Diezani Alison-Madueke
In ba ku manta ba dai a ranar Alhamis din da ta gabata ne shugaban hukumar ta EFCC ya bayyana cewa hukumar ta samu tsabar kudi har dalar Amurka miliyan 9.75 da kuma fam din Birtaniya dubu 750 a gidan tsohon shugaban hukumar man fetur ta kasa NNPC, Mista Yakubu Andrew da ke Kaduna
Bincike dai ya nuna cewa Diezani ta mallaki wannan gida da aka samu tsabar kudaden ne a jihar Lagos kuma a wata unguwa ta masu kudi da ake kira da Banana Island a tsakanin shekarar 2011 zuwa 2012 akan kudi dalar Amurka miliyan 37.5 daga wajen wani kamfanin ginawa da kuma dillacin gidaje mai suna YF Construction Development and Real Estate
EFCC ta ci gaba da cewa wannan nasara da ta samu bankado makuden kudade mallakar gwamnati a hannun tsofaffin jami’an kasar a wannan mako, sakamako ne na alwashin da hukumar ta yi na binciko duk wata kadara ta tsohuwar ministar man fetur din sakamakon binciken da ake yi akanta na yin rub da ciki akan dukiyar kasa da kuma fita da kudade ba bisa ka’ida ba
Gidan na Banana Island gida ne mai hawa 15 da kuma bangarori ko kuma gidaje 18 a cikinsa tare da kuma dakunan sama da a turance ake kira da pent house guda 6. Kuma Diezani ta sayi gidan ne bisa mallakar kamfanin Shell don yin basaja kuma a karkashin kulawar wani Mista Afamefuna Nwokedi na cambar Stillwater da ke Lagos
Ko a bara ma dai sai da EFCC ta kwace wani gida da darajarsa ya kai dala Amurka miliyan 18 a Asokoro, Abuja wanda bincike ya nuna cewa mallakar Diezani ne. Kodayake dai, Diezani ta karyata wannan zargi da aka yi mata