Cin Hanci da Rashawa

EFCC TA NA BINCIKEN BIDIYON GANDUJE A LONDON – MAGU

Kamar yadda za a gani a wannan bidiyon da ke kasa, Mallam Ibrahim Magu, shugaban Hukumar EFCC ya ce daya daga cikin dalilan da ya sa ya kawo ziyara London a makon da ya gabata shine domin ya kudanar da binciken kimiyya, wato forensic analysis, a kan bidiyoyin da ke nuna Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya na karbar wasu kudade da a ke zargin cewa cin hanci ne.

Magu ya fadi hakan ne yayin da ya ke ba da amsa akan tambayar da na yi masa akan bidiyoyin bayan ya gabatar da lacca a kan yaki da cin hanci da rashawa a Afirika a Jami’ar Queen Mary University of London ranar juma’ar da ta gabata. Bayan na ja hankalinsa ga wani ruhoto da jaridar Premium Times ta buga kwana daya kafin zuwansa wanda a ciki aka ruwaito shi yana cewa ba za su binciki Ganduje ba sabo Gwamna mai ci wanda ya ke da rigar kariya, kuma maganar ta na gaban Kotu, sai Magu ya ce: “Ina aiki a kan shi anan (wato London). Ina aiki a kan shi anan. Daya daga (ba a ji da kyau) shine mu yi binciken kimiyya (wato forensic analysis) akan abinda ke dauke a cikin bidiyon.

Wannan ya ci karo da bayanin da na yi da farko cewa Magu ya ki cewa zai binciki Ganduje. Hakan ya faru ne saboda ban ji wannan bangare na amsarsa ba saboda hayaniyar da ake a gurin taron kamar yadda za ku ji a bidiyon ma. Sai yau da na saurari bidiyon a gida, na fahimci abinda ya ce.

Haarun

Haruna Lawan Usman is a certified Animal Health and Production Technologist, with more than 4 years experience in Animal Health and Production Technology.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: