Labarai

EFCC ta kama miliyoyin daloli a gidan tsohon shugaban NNPC

An sha samun badakalar kudi a kamfanin mai na Najeriya
Shugaban riko na hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta Najeriya, Mista Ibrahim Magu, ya shaida wa majalisar wakilan kasar cewa sun samu kusan dala miliyan 10 da kuma fam 750,000 a gidan tsohon shugaban kamfanin mai na NNPC, Mista Andrew Yakubu, a yayin da suka kai wani samame.
Shugaban hukumar EFCC din ya yi wannan bayani ne yayin da yake kare kasafin kudin hukumar na bana a majalisar.
Dama dai Mista Yakubu yana fuskantar shari’a kan zargin halatta kudin haram.
An samu kudin ne a gidan Mista Yakubu da ke Kaduna, kuma su ne kudi mafi yawa da hukumar ta kama a baya-bayan nan.
Yawan kudin idan aka mayar da su kudin Najeriya sun kai naira biliyan uku.
EFCHakkin mallakar hotoEFCC
“Mun kai samame gidansa kuma mun gano tsbar kudi dala miliyan tara da dubu dari bakwai da dubu biyu. Haka kuma mun gano kusan fam dubu dari bakwai da hamsin na tsabar kudi,” inji Mista Magu.
Mista Magu ya kuma shaida wa majalisar cewa hukumar ta samu kusan naira biliyan daya da rabi a gidan wani ma’aikacin gwamnati, a cikin makonni biyun da suka gabata.
Ya ce hukumar ta kwato kusan naira biliyan biyu da fiye da dala miliyan takwas da kuma sama da fam miliyan 29 da euro 12 tsakanin watan Janairu zuwa Disambar shekarar 2016.
Mista Yakubu ya rike mukamin shugaban NNPC ne daga shekara ta 2012 zuwa 2014.