Hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC a yammacin yau ta kama mataimakin daraktan yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyar PDP, Kabiru Tanimu Turaki (SAN). Kakakin jam’iyar PDP, Kola Olobgondiyan ya bayyana cewa, hukumar ta gayyaci Kabiru Turaki daga bisa ni da rikeshi ta ki sakinshi.
Turaki dai Babban Lauya ne a kasar nan, sannan ysohon minista ne a lokacin mulkin PDP kuma daya daga cikin wadan da su ka yi takatan shugabancin Najeriya a jam’iyar PDP a 2018.
Jam’iyar PDP dai ta yi Allah wadai da wannan abin da hukumar EFCC ta yi wa daya daga cikin ‘ya’yanta. PDP ta zargi shugaban kasa da kuma jam’iyar APC da yin amfani da karfin mulki domin wulakanta ‘ya’yanta domin sauke fushinta a kamsu na kin amincewa da sakamakon zabe da su ka yi. Daga karshe ta bukaci EFCC da ta yi gaggawan sakin Kabiru Tanimu Turaki.
Har yanzu dai ba abin da aka ji hukumar ta EFCC ta ce dangane da kama Lauyan.