-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

EFCC Ta Gargadi ‘Yan Canjin Kudi A Najeriya


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Magu ya zargi wadansu ‘yan siyasa da masu canjin kudi da hadin baki wajen karkatar da kudin gwamnati

Mukaddashin Shugaban Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati Ibrahim Magu ya gargadi masu canji kudi da su daina taimaka wa harkokin cin hanci da rashawa da wadansu ‘yan siyasa suke yi a kasar.

Shugaban ya ce hukumar za ta gurfanar da duk wani dan siyasa ko banki da aka samu laifin taka dokokin hada-hadar kudi a kasar, kamar yadda aka bayyana a wata sanarwa da hukumar ta aike wa BBC.

Ya bayyana hakan ne lokacin da shugabannin kungiyar ‘yan canjin kudi ta Najeriya (ABCON) suka kai masa ziyara a hedkwatar hukumar da ke Abuja ranar Laraba.

Shugaban ya zargi wadansu ‘yan siyasa da masu canjin kudi da hadin baki wajen karkatar da kudin gwamnati.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 659

- Advertisement -

Daga nan ne shugaban kungiyar Alhaji Aminu Gwadabe ya yaba da shugabancin hukumar kuma ya ce wadansu mambobinsu marasa rijista ne suke harkokin da suka saba wa doka.

Har ila yau, ya ba da tabbacin cewa “kimanin mambobin kungiyar ABCON masu rijista 5000 ne suke taimaka wa hukumar EFCC wajen yaki da cin hanci da rashawa a kasar.”

Ya kuma ce akwai “kimanin ‘yan canji 100,000 wadanda ba su da rijista a Abuja kawai, kuma su ne suke ba ta mana suna.

“Muna bukatar hada karfi da hukumar EFCC wajen yaki da wadannan bata garin.”

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: