Labarai

EFCC Ta Gabatar Shaidu, Tare Da Wasu Hujjoji Akan Tuhumar Da Akewa Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa

EFCC Ta Gabatar Da Mai Shaida Na Shida, Tare Da Wasu Hujjoji A Sharia’r DA Ake Wa Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Saboda Zambar Naira Biliyan Daya Da Miliyan Dari Uku Kotu ta ci gaba da sauraran tuhumar da Hukumar EFCC ke ma

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido tare da ‘ya’yansa biyu Aminu da Mustapha, sai Aminu Wada Abubakar , da kamfanin Bamaina Holdings da na Speeds International, a yau Jumaa, biyar ga watan Nuwamba, 2021 a wata badakala ta kudi Naira biliyan daya da miliyan dari uku da hamsin a gaban mai sharia Ijeoma Ojukwu ta babbar kotun tarayya, Abuja inda

hukumar EFCC ta gabatar da shaida ta shida, Mercy Titus, wata kwararriyar mai kutse a intanet kuma jamiar hukumar EFCC.

Titus ta fadawa kotu cewa, ayyukanta sun hada da bincike da gano wasu abubuwa da aka boyeko aka lalata musi4amman a cikin na’urori masu kwakwalwa da suka hada da wayoyi, da sauran abubuwan ajiye bayanai na zamani don dawo dasu ko da kuwa sun bata ko an goge su da kuma da tabbatar da sahihancin su da ganin cewa ba’a lalata su ba.

Don karanta karashen labarin da sauran labaran EFCC, ku ziyarci sashen intanet na EFCC a www.efccnigeria.org.

About the author

Haarun

Haruna Lawan Usman is a certified Animal Health and Production Technologist, with more than 4 years experience in Animal Health and Production Technology.

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement