Labarai

Duk Wanda Yayi Goyon Biyu Ku Harbeshi – Gwamnatin Zamfara

Gwamnatin zamfara ta fitar da jadawalin sababbin dakoki a jahar domin magance rashi tsaro da jahar take fama dashi.

Gwamnatin ta fitar da wannan labarinne ta hannun me watsa labaranta na jahar, inda ta bawa shugaban yan sandar jahar umarnin harbi ga duk wanda yayi goyon biyu a mashin akatsai dashi bai tsaya ba a harbeshi tare da wasu dokoki.

Gasu kamar haka

Ta hana goyon mashin

Ta hana cin kasuwar kauye wace akeyi duk sati

Ta hana jigilar shanu a mota

Ta hana diban kayan abinci wanda idan akai bincike ba a samu kwakkwaran daliliba zai akai abincin gidan marayu da gidan ajiya.

Ta sanya dokar hawa mashin da kake daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yanma a cikin kauye, cikin birni kuwa daga karfe 6 na safe zuwa 8 na dare.

Dama wasu sauran dokokin.

Shugaban yan sandar jahar ya roki al’ummar jahar da subi doka su zauna lafiya.

Allah ya karamana zaman lafiya a wannan kasa tamu baki daya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: