Madugun kungiyar ‘yan tsagerun nan masu fafitikar kafa kasar Biyafara ta IPOB, Mista Nnamdi Kanu ya jaddada cewa duk wanda ya yi yunkurin sake kama shi zai mutu inda ya nuna cewa babu wanda ya isa ya dakatar da batun kafa Biyafara saboda sako ne daga Ubangiji.
Ya ce, ‘ a shaidawa Shugaba Buhari cewa ina nan cikin garin Aba kuma ba zan yi gudun hijira ba saboda wasu jahilai sun ce za su zo su kama ni, to ina jiransu kuma Ina tabbatar masu ba za su bar garin Aba da ransu ba”.
A kwanan nan ne dai, Ministan Shari’a ya nuna cewa za a sake kama Shugaban kungiyar ta IPOB saboda ya karya dukkan sharuddan da kotu ta gindaya masa kafin a bayar da belinsa a ranar 25 ga watan Afrilu.
Source in rariya
Add Comment