Labarai

Duk Mai Cewa Farin Jinin APC Ya Ragu, Ya Bari Zaben 2023 Ya Zo, Cewar Gwamna Masari

..Buhari ya yi hakuri da mutane da yawa

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya ce shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi hakuri da mutane da dama a kasar.

Cikin wata hira da gidan talabijin na TVC Masari ya ce ya yin da wasu shugabanni suka gaza jurewa sukar da ake musu, Buhari ya jima yana hakan.

Masari ya kara da cewa Buhari bai gaza ba wajen cika duka alkawuran da ya dauka yayin yakin neman zabe, yana kuma bayyana jam’iyyar APC a matsayin abar dogaro ga ‘yan Najeriya.

“Duk wanda yake cewa farin jinin jam’iyyar ya ragu to ya bari a zo lokacin zabe. Kuma yadda APC ke kara amsar mutane ya nuna wannan zargin ba daidai ba ne.

“Ina ganin har yanzu APC ce jam’iyyar da ta fi ko wacce karfi,kuma wadda za a iya dogara da ita a Najeriya a yau.” in ji Masari

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: