Kannywood

Duk fim din da Nafeesat ta yi kuka a ciki haka kawai sai inga ina hawaye – Hajia Mama

Shahararriyan yar wasan fina-finan Hausa Nafeesat Abdullahi ta gama shiri tsaf don sako wa masoyanta da masoyan fina-finan sabuwar film da ga ledar ta fes-fes mai suna KARMA.

Nafeesat dai shahararriya ce wajen shirya musamman fina-finan soyayya da ban tausayi.

Wata masoyiyar Nafeesat, Haj. Mama ta shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa “duk fim din da naga Nafeesat ta na kuka sai nayi kuka nima. Abin kamar almara wallahi. Allah kuma yayi duk sonta sa nakeyi Allah bai taba sa mun gaisa ba ko ta waya ne.”

Masoya dai na nan suna jiran wannan fim na KARMA.

 

Source PMHausa