Fitaccen dan siyasar nan kuma tsohon dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano a karkashin babbar jam’iyyar adawa ta PDP a shekarar 2019, Aminu Abdussalam ya zargi ‘yan fanshon jihar Kano da nuna rashin godiya ga Allah.
Abdussalam ya ce ‘yan fanshon da suka kai karar tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso zuwa ga hukumar EFCC ba su da godiyar Allah ko kadan kuma basu kyauta ba.
A lokacin Kwankwaso ne ‘yan fansho suka ji dadi suka kuma samu walwala sosai, domin a lokacin ne yayi musu karin kudi har naira dubu biyar (N5,000). Amma wai yau sune suka kai shi kara gaban hukumar EFCC.
Duk dan fanshon da bai godewa Kwankwaso ba butulu ne kuma wutar jahannama ce makomar sa, sabodda Kwankwaso ya yi iya bakin kokarinsa. Daya bayan daya za a dinga jefa su a Jahannama saboda rashin godiyar Allah da suke da ita..
A cikin makon da ya gabata ne dai jaridar Premium Times ta ruwaito cewa hukumar EFCC ta aikawa da Sanata Kwankwaso sammaci.
Duk da dai cewa Kwankwaso bai kai kanshi ga hukumar ta EFCC ba, amma wasu bayanan sirri suna nuna cewa ‘yan fansho na jihar Kano ne suka maka shi gaban hukumar domin yaje yayi bayani dangane da kudaden fansho na jihar a lokacin da yayi gwamnan jihar.
Hukumar ta EFCC na zargin Kwankwaso da handame wasu makudan kudade na ‘yan fansho a lokacin da yake mulki a jihar.
Mutane da dama na ganin cewa wannan lamari na da nasaba da wata makarkashiya da ake so a yiwa tsohon gwamnan don a kakaba masa laifi, ganin yadda matar gwamnan jihar Hafsat Ganduje da dan ta suke faman tafka rikici kan harkallar wasu makudan kudade.
Wannan dalili ne ya sanya suke ganin aka maka Kwankwaso gaban hukumar EFCC.
Add Comment