Kannywood

Duk Da Ni Bayerabiya Ce, Ban Taba Samun Bambancin Wariya A Masana’antar Kannywood Ba, Cewar Rahma MK

…ba zan iya auren saurayi dan shekara 25 ba, duk da shekarata 32 a duniya
Daga Jamilu Dabawa, Katsina
Sunana Rahma MK Sulaiman , wadda aka fi sani da Hajia Rabi Bawa Mai Kada. Ni Bayarrabiya ce haifaffiyar garin Zaria jihar Kaduna. Na yi aure a garin Jos, ina da yara guda biyu, ina zaune a jihar Kano, shekaruna 32 da biyu a duniya.

Da aka tambayeta ko yaushe ta fara harkar fim, sai ta kada baki ta ce na fara fitowa a fim a shekarar 2013 kuma fim dina na farko guda biyu aka yi a lokacin daya. Sunan fina-finan akwai “Kin Ci Amanata” da kuma “Nisan Kiwo”

Yadda aka sanya ni was an mai dogan zango, da aka zo gwajin murya ko zan iya watau (audition) sai aka ce sai na kara kiba, daman ina da jikin kiba na ci gaba ciye-ciyen abinci masu sanya kiba. Yanzu kuma da aka zo karo na shidda an ce ana son in rage kibar, har na fara shirye-shiryen hakan.

Ko mi ya fi burge Hajia Rabi Bawa Mai Kada, sai ta ce abinda ya fi burge ni shi ne in tashi da safe in kira mamana ko ta kirani in ji tana zazzaga mani albarka. Abinda kau ya fi ba ni haushi da wuri yake taba ni akwai karya da yaudara da kuma munafurci.

An tambayi Rahma MK ko tana iya auren matashi dan shekara ashirin da biyar, sai ta furta cewa ban da dai aure, sai dai ko abotaka mu rinka gaisawa, amma gaskiya banda maganar aure. Saboda ina da yara kuma ba zan so yarana su raina mijina ko dan yana da karancin shekaru ko dan sun ganshi karami. Ko yaushe za ta yi aure? Sai ta ce ina nan ina addu’a kuma masoya su taya ni addu’a, idan Allah ya kawo yau ko gobe zan yi.

Galibi ana kallon yan fim da rashin kamun-kai ko mi za ta ce “shi lalatacce, lalatacce ne ko a ina yake ba a kannywood kadai ba ne, a gida ko a unguwa ko kuma a gari ne ko ma’aikata musamman wadda ta hada maza da mata ana iya samun kowa a ciki. Da aka tambaye ta ko ta taba fuskanta wariya kasancewarta Bayarrabiya a masana’antar Kannywood kuwa? Sai ta kada baki ta ce “to gaskiya ban taba samun wariya ba ko sau daya, ina yabon masana’antar Kannywood , saboda ban taba jin an ce ba za’a sanya Rahma fim ba, saboda tana Bayarrabiya ba.

Daga karshe ina mika godiya ga mahaifana da tsohan mijina da kuma Dokajin Kano da matarsa da kuma masoyana duk inda suke a fadin duniya ina masu fatan alheri.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: