Duk Abinda Aka Damka A hannun Atiku, Ba Ya Taba Lalacewa -Dogara

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Kakakin majalisar wakilai a Najeriya, Honarabul Yakubu Dogara ya ce duk abinda aka damka a hannun dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar baya taba lalacewa.

Jaridar The Cable ta rawaito cewa Dogara ya yi wannan furucin ne a ranar Asabar wajen walimar daurin auren dan uwansa Hassan Ishaya da amaryarsa Mafeng a babban birnin tarayya, Abuja.

Talla

Kakakin majalisar ya ce Atiku Abubakar ne dan takarar da zai fitar da Najeriya daga kangin talauci da ya yi mata katutu a halin yanzu.

Dogara ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su zabi mutumin da ya samu kwarewa da horaswa da zai iya kawo gyara a kasar.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

Yace “Idan ka dubi Wazirin Adamawa a matsayin shugaba a Najeriya, kuma ka sake bincikawa a duk lunguna da sakon Najeriya ba za ka taba iya kidaya mutanen da Atiku ya gina ba.

“Sirrin shine duk abinda ke sanya a hannun Waziri, abun baya tabarbarewa. Idan ka saka ilimi a hanunsa, zai zama jami’a. Shine ya kafa daya daga cikin jami’a mafi inganci a Najeriya. Idan ka saka kudi a hannunsa, ba zai tabarbare ba.” a cewarsa

Dogara yaci gaba da cewa “Wadanda ke kishin cewa duk abinda ka saka a hannunsu yana tabarbarewa za su ta kokarin sukar sa amma maganar gaskiya shine da wahala ka saka abu a hannun Atiku abin ya lalace.

“Saboda haka idan muna da wayo a kasar nan yanzu da abubuwa da dama ke tabarbarewa, kamata yayi mu damka kasar a hannunsa. Ina fada muku idan muka saka tattalin arzikin Najeriya a hannunsa, kowa na iya zuwa ya yi barci, za ku ga abinda zai faru,”inji Dogara.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: