Labarai

Dole Kowane Mutum Ya Biya Harajin ₦2000 Duk Shekara – Gwamnatin Katsina

Wajibi ne ga kowane Mutum da ya kai shekara Goma Sha Takwas 18 zuwa sama a Katsina ya biya harajin Naira Dubu Biyu 2,000….Masari

Gwamnatin Jihar Katsina ta amince a zaman Majalisar zartarwa da tayi jiya Laraba 07/07/2021 cewa kowane mazaunin jihar Katsina da ya kai shekara Goma sha Takwas zai rinƙa biyan harajin Naira Dubu Biyu 2,000 a duk shekara Matsayin abunda aka kira “Harajin Raya ƙasa”.

Kwamishinan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki na Jihar, Faruq Lawal Jobe ne ya bayyana haka a ranar Larabar nan bayan kammala taron majalisar Zartaswar jihar.

Joɓe ya bayyana cewa harajin ya shafi ma’aikatan Gwamnati dama wanda ba ma’aikacin Gwamnati ba, mai Sana’a da ma wanda baya sana’ar, Ɗan jiha da ba Ɗan jiha ba duka ya wajaba ya biya harajin madamar dai yana zaune a cikin jihar.

Sai dai dokar harajin tayi rangwame wajen Mata dokar ta ce Macen da take aikin albashi ita ce kaɗai za ta biya harajin, Mata na cikin Gida kuma Mazajen su sun ɗauke masu.

Harajin dai wanda aka kira da “harajin raya kasa” kwamishinan ya ce an tsara yadda za’a rinƙa karbarsa inda ya ce sun bullo da wani tsari da zai ɗauki bayanan yawan dukiya da hoto da katin ƙuri’a ko katin zama ɗan ƙasa da lambar BVN da kuma waɗanda ke makwabtaka da wanda ya biya harajin.

A ɓangaren jangali kuma Jobe ya ce duk wanda ya mallaki shanuwa zai biya Naira Ɗari Biyar ne a kan kowane sa ko shanuwa a duk shekara.

Haarun

Haruna Lawan Usman is a certified Animal Health and Production Technologist, with more than 4 years experience in Animal Health and Production Technology.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: