Dokar hana yin fim kan aikata ta’asa: Afakallah ya biyo layin hauka, inji Falalu Ɗorayi

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

- Advertisement -

FITACCEN jarumi, furodusa kuma darakta Falalu A. Ɗorayi, ya yi fatali da dokar nan da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta ƙaƙaba wa Kannywood wadda ta haramta shirya fim kan ayyukan ta’asa irin su kidinafin, shaye-shaye  da ƙwacen waya.

Idan kun tuna, shugaban hukumar, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallah), ya bayyana wa mujallar Fim a ranar Talata da ta gabata cewa gwamnati ta ɗauki wannan matakin ne domin kare mutunci da al’adar mutanen Kano.”

Ɗorayi, wanda ya na ɗaya daga cikin masu shirya fim da ake ganin wannan dokar za ta shafa, ya faɗa wa mujallar Fim cewa kwata-kwata Afakallahu bai yi aiki da hankali ba kafin ya yi wannan dokar.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 1,306

“Mutumin nan ya na tafiya ne kawai ya na ta hauma-hauma,” inji shi.

A hirar musamman da ya yi da mujallar Fim kan sabuwar dokar ta Afakallahu, daraktan ya ce, “Abin tambaya a nan shi ne da me ya dogara da zai ɗauki wannan mataki duba da cewar komai in za a yi ana fara tattara masu ruwa da tsaki kan lamarin ne a yi magana da su cewa ga wani abu da gwamnati za ta yi a matsayin ku na wanda mu ke tare da ku na cewa finafinai da ake ko a juya akalar su a gyara a ɗan daina saboda abin ya fara ta’azzara? Amma kai-tsaye ka ce za ka yanke hukunci a matsayin ka na gwamnati, ya zama kamar mulkin soja kenan ko?

“Ba wata doka da ta ce ba za a nuna fim na shaye-shaye ba, ba za a haska fim na abin nan ba.

“Ai har yanzu ana yin fim ɗin Amurka, kuma har gobe su na yin fim a kan masu tada ƙayar baya. Fim ɗin 11 ga Satumba da aka yi na kai masu hari a kan Pentagon da waye-waye har gobe su na fim a kai da yadda su ka tsara abin da yadda su ka je su ka kai masu harin, har gobe ana yi.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.