Da Duminsa: a karon farko Dikko Radda ya yi sabbin nade-nade daga ciki har da Arc Ahmed Dangiwa a matsayin sakataren gwamnatin jihar Katsina
Daga Ibrahim M Bawa
A ‘yan awanni kadan da rantsar da sabon gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Radda, har ya gudanar da wasu sabbin muhimman nade-nade.
Daga cikin nade-naden da ya yi a yau Litinin, akwai Arc Ahmed Musa Dangiwa a matsayin sakataren gwamnatin jihar Katsina, a inda kuma ya nada Alh Jabiru Tsauri a matsayin shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, yayin da Barr Muktar Aliyu Saulawa a matsayin mataimakin shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Katsina, sai kuma Alh Abdullahi Aliyu Turaji a matsayin sakatare na musamman a ofishin gwamma
Haka kuma gwamna Radda ya nada Mallam Maiwada Danmalam a matsayin Darakta Janar na Media, sai kuma Ibrahim Kaula Mohammed a matsayin babban sakataren yan jaridu na gwamna, da Malam Miqdad Isah a matsayin babban mai taimakawa gwamna a kafafen sadarwar zamani (Digital Media) sai kuma Abubakar Badaru Jikamshi Babban mai taimakawa na musamman kan abin da ya shafi kafafen sadarwar da ake wallafawa da kuma na kallo da sauraro (Print and Electronic Media)
Sauran nade-naden kamar yadda Katsina Daily News ta ga sanarwar da Isah Miqdad Saude babban mai taimaka wa gwamnan a kafafen sadarwar zamani ya fitar, Dikko Radda ya aminta da nada Alh Bishir Maikano a matsayin babban protocol a ofishin mataimakin gwamna, da Hassan Ibrahim Danhare a matsayin babban mai taimawa mataimakin gwamna a ayyuka na musamman, da kuma Ahmed Rabi’u a matsayin mai daukar hoto na musamman a ofishin gwamma.
Daga karshe gwamman ya taya wadanda ya yi wa sabbin nade-naden farkon murna da fatan Allah Ya taya su riko
Add Comment