Siyasa

DEMOKARADIYYA: Shugabancin Gwamna Buni A Jam’iyyar APC Ya Sauya Salon Siyasar Nijeriya

Daga Haruna Sardauna

A tsarin Demokaradiyya Shugaban jam’iyyar da take mulki a kasa, shine jagoran siyasar kasa, duk shugaban jam’iyyar da take mulki zakaga suna amfani da Izzar mulki, kuma a tsari na Demokaradiyya amfani da Izzar-mulki shine yake haifar da rikicin Siyasar cikin gida da harzika Yan jam’iyyar adawa, wannan shine Babbar matsalar da yake haifar da rikicin Siyasa a Najeriya.

Saide Shugabanci Gwamna Buni a Jam’iyyar APC mai mulki tazo da sabuwar salon siyasa, wanda ta chanza tsarin Demokaradiyyar Najeriya ta fuskoki da dama, gudanar da jam’iyyar cikin ruwan Sanyi, lalla6a da rarrashin mabiya, babu nuna Izzar-mulki, babu karfa-karfa, babu nuna Isa, babu nuna karfin iko, tsarin siyasar Gwamna Buni ta Sanyaya Guiwar yan jam’iyyun adawa saboda shugabancin shi ta banbanta da sauran shugabannin da suka jagoranci jam’iyya mai mulki a tarihin siyasar Najeriya.

Zurfin Kwarewar Gwamna Buni a siyasa, ya haifar da daidaito da fahimtar juna tsakanin jam’iyya mai mulki da jam’iyyun adawa a Najeriya, duk zafin adawar jam’iyyar adawa ta PDP jikinsu yayi sanyi kan kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki saboda tsarin mulkin-Demokaradiyyar Gwamna Buni ta gabatar da tsarin “Siyasa Bada Gaba ba” Shugabannin Siyasar karkashin jam’iyyar APC dana Babbar jam’iyyar adawa ta PDP sun iya mu’amalantar junan su cikin Mutuntawa.

A karkashin jagoranci gwamna Buni a Jam’iyyar APC mai mulki, aka daina yin shunen EFCC da ICPC a shugabanni da masu ruwa da tsaki a jam’iyyun adawa ko a masu kalubalantar tsarin gwamnatin APC, a lokacin gwamna Buni aka daina cin mutuncin manyan Mutanen da basa biyayya a Gwamnati, hakan yasa da yawa sun ajiye Makaman yakin su na kalubalantar gwamnati shugaba Muhammadu Buhari.

Bada shugabancin jam’iyyar APC na kasa a Gwamna Buni, ta fito da wani boyayyar Baiwar Gwamnan, yanayin kware da baiwar Hon. Mai Mala Buni, yasa masu hasashe da buga alkaluman siyasa, sun sanya shi a sahun gaba cikin matasan yan Siyasar da zasu iya shugabanci Najeriya, Gwamna Buni shine Tauraron Demokaradiyyan Najeriya a yau, wanda ya zama zakarar gwajin dafi a tsakanin yan tsofi da sabbin yan Siyasar Najeriya.

Social and Welfare Director
North-East APC Social Media Forum

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement