Labarai

Dawowar Zaura Zuwa Jam’iyyar APC Ya Sanya Tsoron Dushewar Hasken Yau A Idanun Saura

Daga Sharif Aminu Ahlan
Zan faɗa babu shakka ko fargaba a wannan wuri a kuma wannan lokaci ba tare da kokwanto ko waraki ba, dawowar A.A Zaura zuwa cikin jam’iyyar APC tare da gagarumin gangamin karɓar sa a hukumance a ranar Asabar, 12 ga watan June, 2021 haƙiƙa ya tada gashin ido tare da sanya bakuna yin tsokaci da martani da fassara waɗanda su ka mamaye kafafen watsa labaranmu na Redio da sauran kafafen sadarwa na zamani da gidajen jaridu.

Kamar yadda ake tsammani a haƙiƙa, duk wani babban gangamin karɓan sabbin ƴan jama’iyya zai ƙara yawan ƴan jam’iyya da ƙara ɗaga girma da nauyin jam’iyyar tun daga Jiha har ƙasa, tasirin ba wai zai tsaya ne ga iya ƙananan hukumomi 44 ba, zai shafi jam’iyyar ne gabaɗaya daga Jiha har ƙasa.

Wani ƙarin albarka da jam’iyyar ta samu shi ne kasancewar dubban membobin ƙungiyar Kwankwasiyya da su ka halarci wurin kuma su ka yanke shawarar watsi da jam’iyyarsu gami da komawa cikin jam’iyyar APC, hakan ya faru ne sanadiyyar imani da ƙarfin gwiwa da amanna da mutumin da aka shirya wannan gangami mai cike da tarihi domin girmama shi.

Ba shakka mutumin ba kamar sauran gama-garin ƴan siyasa ba ne, amma babban ɗan siyasa ne mai ƙwarewa da ɗumbin mabiya a duk jam’iyyun adawa a Jiha da ƙasa gaba ɗaya. Idan har kasancewarsa za ta ja hankalin ƴan amutun kwankwasiyya waɗanda su ka ba da jini da rayuwarsu akanta su ke binta a makance da canjin tunani su ka watsar su ka dawo jam’iyyar APC, ba shakka buɗaɗɗen al’amari ne kan muhimmanci da amfanin mutumin sannan kuma albarka ne kuma kariya ne sannan garaɓasa ce.

Duk wannan su na bayyana amfanin mutumin a siyasa ga duniya. Sannan kuma baiwace ga cancanta ta musamman ga mutumin da Allah ya halitta da kamala da nagarta da albarka. Mutum ne wanda aka sani da ayyukan jinƙai da taimakon al’umma musamman marasa ƙarfi da mabuƙata. A kowane lokaci ya na sadaukar da dukiyarsa da abin da ya samu domin samarwa al’umma kykkyawar rayuwa. Ba mu yi bayani irin ƙarfin basira da kaifin ƙwaƙwalwarsa kan lissafin siyasa ba. Mutum ɗan kasuwa mai kykjyawar zuciya da tsoron Allah da kiyaye dokokinsa. Mutum ne mai sauƙin kai da tawali’u, kyawawan ɗabi’o’in da su ka sanya al’umma da dama su ka kasance tare da shi.

Haƙiƙanin gaskiya dukkan membobin jam’iyya sun yi maraba da shigowarsa cikin jam’iyyar. Sai dai abin takaici da ɗaure kai da mamaki wasu daga cikin manya su na tsoron abin da ba su sani ba. Kamar kowacce jam’iyyar siyasa, membobinta a kowane lokaci su na da ƴanci da damar neman kowane irin matsayi ko muƙami wanda hakan shi ne ajin farko na tushen samar da dimokaraɗiyya. Jam’iyyar APC ba ta sha bamban da sauran jam’iyyu ba.

Dubban al’umma da buƙatun kai su na kare matsayi ko muƙamin da su ke son nema a lokacin zaɓe. Da dama su na da burin neman takara tun daga kan kansila har zuwa gwamna ko ma shugaban ƙasa. Akwai waɗannan mabambantan hasashe da fassara a tsakanin masu biyayya wa jam’iyya wadda waɗansu su ke tunanin mutumin zai nemi matsayin gwamna, matsayin da ya nema a ƙarƙashin jam’iyyar GPN da ya baro.

Sai dai duk wannan hasashe ne da canki-canka, domin mutumin bai bayyana haƙiƙanin kujerar da zai nema a lokacin zaɓe ba. Labarai su na fitowa daga majiya mai tushe cewa manyan ƴan jam’iyya da ke da burin neman ganin sun gaji gwamna Ganduje ƙila sun tsorata da shigowar mutum na mutane wanda ya ke da kykkyawar alaƙa da jama’a wanda ka iya zamewa barazana a gare su.

Tsoronsu shi ne sanin hali, da bibiyar tarihi, da ƙwarewa kan wasan siyasa da ƙulle-ƙullenta. Sai dai waɗanda su ke haɗa shi da kujerar majalisaar tarayya su na mafarki ne. Ya yin da wasu su ke ƙarfafa hasaahensu kan siyasar ƙasa ya kasance sabon ɗan sarkin siyasar Jiha bai zama lallai ya nemi kowane irin muƙami ba amma ya na da ɗumbin mabiya ga ɗan takarar da zai marawa baya a matakin zaɓen gwamna da shugaban ƙasa.

Zai iya kasancewa gaskiyar batu shigowar ɗumbin matasa da ƴan siyasa masu ƙarfi cikin jam’iyyar gwamnati, ba abin faɗi bane kawai ko karɓa da ba da masauƙi da murna ba. Amma kuma zai girgiza jiga-jigan ƴan siyasa masu burin cigaba da damawa yadda su ke so domin cimma burukansu na ƙashin kai. Tun asali zai sanya tsoro kan abin da zai je ya zo a zukatan wasu.

A yanzu ya zama wajibi mu maida hankali wajen ririta da aminta da ribatar wannan babbar garaɓasa kana kuma babbar kadara da ta sauka. Dangane da abin da ya shafi dama da ƴancin da kundin tsarin mulki ya ba shi na neman wani matsayi, lokaci ne kaɗai zai nuna.

Ahlan babban haziƙi, sadaukin mayaƙi na gwamna Ganduje daga Jihar Kano.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: